Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana yawan 'ya 'yan da yake so ya haifa.

Share:
- Dan kwallon Duniya Ronaldo yace burin sa ya samu 'Ya 'ya 7 a rayuwa

- Tauraron Dan wasan yace yana da bukatar samun 'ya 'ya 4 nan gaba

- Kwanan nan dai Dan wasan kwallon kafan ya samu tagwaye tubarkalla

Mun samu labari cewa Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana yawan 'ya 'yan da yake so ya haifa. Dan wasan yadda yake goya lamba 7 haka yake so ya goya 'ya 'ya 7.Cristiano Ronaldo da tagwayen sa
Babban Dan wasan yana da 'ya 'ya 3 yanzu wanda babban yake da shekaru 7 sannan kuma ya samu tagwaye kwanan nan. Ma'ana dai Dan wasan na kasar Portugal na bukatar karin 'ya 'ya 4 har yanzu.

Yanzu haka dai mun ji cewa Budurwar Cristiano Ronaldo watau G. Rodriguez tana da ciki yanzu haka. Sai dai 'ya 'yan na 'Dan wasan ban da ba a san uwar dukkan su ba kusan mata dabam su ka haife su. Ronaldo Jr. yana bukatar ayi masa 'yan kannai 6.

Kwanaki dai Dan wasan na Real Madrid din ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve daga Kasar Amurka.

No comments