Majalisar Dattawa ta yi tir da kamfanin sadarwa na MTN

Share:
Kamfanin sadarwa na MTN ya fusata majalisar dattawa sandiyar makudan kudi da kamfanin ya fitar da Najeriya wanda hakan ya janyo majalisar take bukatar a horar da bankin Stanbic IBTC

A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar dattawa ta bayyana cewa akwai kimanin kudi na na dalar Amirka biliyan 13.92 da kamfanin sadarwa na MTN su ka fitar daga kasar nan tsaknin 2006 zuwa 2016.


Majalisar Dattawa ta yi tir da kamfanin sadarwa na MTN
Majalisar ta tabbatar da wannan laifin ne bayan da kwamitin dattawa sashen harkokin banki, inshora da duk wata ma'aikata dake harkalla da kudi su ka kawo rahoton cewa kamfanin sadarwa na MTN ya karya wata doka ta fitar da kudi daga cikin kasar nan.


Sanatocin sun ce ba shakka wannan karya doka da kamfanin MTN ya yi ya taimaka wajen gurbacewar tattalin arzikin kasar nan da a ke fama da shi a yanzu saboda wannan zunzurutun kudi da kamfanin ya fitar daga kasar nan.

Sun bayyana cewa, a ce kamfani daya ya fitar da wannan makudan kudi wanda hakan zai yi sanadiyar kawo cikas da gurbacewar tattalin arziki tta kasa.

Majalisar ta umarci babban bankin Najeriya CBN, da ya dauki mataki kwakkwara a kan bankin Stanbic IBTC saboda rashin bayyana takardu na kwarai da za su yi nuni a kan wannan kudi da kamfanin na MTN ya fitar.

No comments