Ashe beraye da kwari ne suka hana shugaba Buhari shiga ofishinsa

Share:
- Garba Shehu ya musanta zargin cewar shugaba Buhari bai gama sama samun lafiya ba
- Beraye da wasu Kwari ne suka tafka gagarumar barna a ofishin shugaban kasa
- An kira 'yan 'kwana-kwana' su zo su fidda su
Karshen satin da ya wuce ne Shugaba Buhari ya dawo gida Nigeria, bayan shafe kwanaki 104 yana zaman jinya a birnin Landon. Sai dai bayan dawowar tasa, sai aka ga bai fara aiki a ofishinsa ba, batun da ya sa ake tunanin ko bai warke bane.

Barnar da suka yi ta saka Buhari har yanzu ke aiki a ofishinsa na gida duk da ya dawo - Garba Shehu
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba shehu ya bayar da dalili. A cewar Garba Shehu, beraye da wasu Kwari ne suka tafka gagarumar barna a ofishin shugaban kasar yayin da yake zaman jinya a birnin London kuma ba a ankara da ta'asar da berayen suka yi a ofishin ba sai bayan dawowar shugaban kasar.

Garba Shehu ya musanta zargin cewar shugaba Buhari bai gama sama samun lafiya ba, yana mai ce wa " duk Wanda ya ga shugaba Buhari bayan dawowar sa, ya san ya samu lafiya ". Ya Kara da cewar " shugaban kasa na da ofishi guda biyu ne, daya a gida, daya kuma a waje amma saboda barnar da berayen suka yi a ofishin shugaba Buhari na waje ya sa yake aiki a ofishinsa na gida, kuma tuni a ka ba wa kamfanin julius berger aikin gyaran ofishin shugabab na waje da berayen suka lalata ".

No comments