Da dumin sa! Karanta sakon barka da Sallah da Buhari ya aiko wa yan Najeriya

Share:
Yanzu yanzu ba da dadewa bane ba shugaba Muhammadu Buhari ya aiko wa jama'ar Najeriya musamman ma musulmai da sakon barka da Sallah tare da fatan ayi sallar lafiya cikin ni'ima da salama.
Shugaban ya fitar da sakon ne a cikin wata sanarwa da maitaimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanyawa hannu inda kuma shugaban ya sake isar da dumbin gaisuwar bangajiya da musulman duniya da yanzu haka suke aikin hajji a kasar Saudiya.
Da dumin sa! Karanta sakon barka da Sallah da Buhari ya aiko wa yan Najeriya
Da dumin sa! Karanta sakon barka da Sallah da Buhari ya aiko wa yan Najeriya
NAIJ.com ta samu dai a cikin sakon shugaban ya kuma sake kara jaddada godiyar sa ga yan Najeriya bisa addu'oin su a gare shi da kuma goyon baya.
Shugaban ya kuma bukaci yan Najeriya da suyi koyi da Annabi Ibrahim wajen kokarin dagewa cin jarabawar da Allah zai yi musu su kuma ci gaba da hakurin zama a tare kasa daya.
Daga karshe kuma sai shugaba Buhari din ya kara jadadda aniyar sa ta tabbatar da zaman Najeriya dunkulalliyar kasa tare kuma da kara tabbatar da mulki mai inganci.

No comments