Gwamnatin Saudiyya ta hana mahajjata da dama shiga kasar saboda rashin takardu

Share:
-Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta hana mahajjata sama da N400,000 shiga kasar domin basu cika ka'idojin da suka dace ba
-An tanadar da jami'an tsaro sama da 100,000 domin tabbatar da tsaro yayin gudanar da aikin hajjin
-Duk wanda aka kama yana karya doka zai fuskanci hukuncin tara ko kuma zuwa kurkuku
Wannan sanarwan ya fito ne daga bakin ministan harkokin cikin gida na kasar a lokacin da yake yin jawabi ga manema labarai akan irin shirye-shiryen da kasar takeyi domin karaban mahajjata sama da miliyan 2 wanda zasu zo kasar domin sauke faralin su.
Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta hana mahajjata sama da N400,000 shiga kasar domin basu da ingantatun takardu.
Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta hana mahajjata sama da N400,000 shiga kasar domin basu da ingantatun takardu.
Jami'an kasar sun dauki tsauraran matakai wanda suka hada da aikewa da mutum gidan kurkuku da kuma yankawa mutum tara domin dai a tabbatar da gudanar da aikin hajjin cikin yanayi mai kyau.
A Ranar Talata, ma'aikatan harkokin cikin gidan har ila yau ta sanar da cewa a kala mahajjata miliyan 1.7 daga kasashen waje sun isa kasar kana guda 200,000 yan kasar Saudi Arabia sun iso garin Makka domin shirye-shiryen fara aikin hajjin.
An tanadar da jami'an tsaro sama da 100,000 da su samar da tsaro ga mahajjatan a aikin hajjin wannan shekarar ta 2017.
Jami'in hulda da jama'a na ma'ikatan harkokin cikin gida, Mansour Turki, yace jami'an tsaro sun gano wuraren aijye mutane ba kan ka'ida ba a shekarun da suka wuce.
Turki ya cigaba da cewa jami'an tsaron zasuyi iya kokarin su wurin kiyaye irin cinkinson da ya haifar da rasa rayuka a hajjin shekara ta 2015. Ya kuma yi kira da mahajjata su bi dokokin da hukumar aikin hajjin ta shimfida.

No comments