Kalli hotunan katafariyar matatar mallakin hamshakin attajir Aliko Dangote

Share:
Ministan mai na kasa Emmanuel

Kachikwu ya kai ziyarar gani da ido matatar mai na hamshakin attajirin nan dan Najeriya Aliko Dangote dake jihar Legas, kamar yadda ma’abocin Facebook ya ruwaito.

Majiyar NAIJ.com Buhari Sallau ya bayyana Ministan mai ya samu tarba daga shugaban kamfanin Alhaji Aliko Dangote tare da shugaban kamfanin Devakumar Edwin.


Devakumar ya bayyana wasu daga cikin bayanan kamfanin da suka hada da:

1. Matatar man itace mafi girma a nahiyar Afirka kwata

                  Ministan yayi ziyarar

2. Za’a dinga tace mai daya kai ganga 650,000 a kowanne rana


3. Matar man zata fitar da sinadarin ‘Polypropylene’ tan 750,000

4. Za’a samar da tan 2.8 miliyan na taki

5. Matar man zata samar da iskar Gas da zata iya samar da wutan lantarki a gidaje
                     A yayi ziyarar

6. Za’a dauki ma’aikatan dindin su 1,600, da kuma mutane 100,000 da zasu dinga cin abinci a kamfanin

7. Kamfanin zata tattala ma Najeriya dala biliyan 7.5

8. A shekarar 2019 za’a kammala gina wannan katafaren kamfani
                  Matatar man

A nasa jawabin, ministan man fetur na kasa, ya bayyana cewa gwamnati zata samar da ingantaccen yanayi na yin kasuwanci, musamman na harkar mai, tare da jinjina ma kokarin Alhaji Aliko Dangote, inda ya kara da cewa gwamnati ta dogara akan wannan matatar ta mai domin samun saukin karancin man fetur.


No comments