Kungiyar ASUU ta baiwa gwamnati sababbin sharudda 6 na janye yajin aiki

Share:
Kungiyar ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya sababbin sharudda guda 6 wanda sai ta cika su kafin ta janye yajin aikin da ta shiga makonni biyu da suka gabata.
A ranar Talatar da ta gabata, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Agusta, Ministan aikace-aikace da masana'antu, Dakta Chris Ngige ya roki malaman makarantar ko dan daliban da ba su jiba kuma ba su gani ba.
Hukumar ASUU ta baiwa gwamnati sababbin sharudda 6 na janye yajin aiki
Hukumar ASUU ta baiwa gwamnati sababbin sharudda 6 na janye yajin aiki
A yau ne za a tafka mahawara a zaman tattauna na kusoshin gwamnatin kasar nan wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranta a karo na farko bayan dawar sa daga kasar Birtaniya.
Wannan sharudda shiddan da kungiyar ASUU ta baujuro da su ba sa cikin bukatan da ta ke nema daga wajen gwamnati a baya.
Ga jerin sharuddan guda 6 da sanadinsu.
1. Gwamnatin tarayya ta yi gaggawar amincewa da biyan cikon kudin albashin jami'o'i
2. Jami'o'i su rinka gudanar da al'ammuran haraji na kudi da kansu kuma a ware su daga cikin asusun kasa guda.
3. Kula da kudaden da suka shiga asusun jami'o'i ba tare da sanya hannun gwamnati ba.
4. Tabbatar da yarjejeniyar lokacin ajiye aiki na Farfesoshi kamar yadda ta bukata a shekarar 2009.
5. Biyan albashi daidai da na ma'aikatan jami'o'i ga malaman makarantun firamare na jami'o'i.
6. Amincewar gwamnatin ga jami'o'i su kafa kamfanin biyan fansho karkashin kulawar jami'o'in.

No comments