Za a samar da motoci ma su amfani da wutar lantarki a Najeriya a 2018

Share:
Abu namu maganin a kwabe mu, domin kuwa nan ba da jimawa ba za a fara shigo da motoci masu amfani da wutar lantarki a nan kasa Najeriya domin rage dogaro da man fetur da ake kokarin yi a kasashen duniya baki daya
Wani kamfanin kera motoci, Nigus Enfinity, ya ce zai gabatar da motoci masu amfani da wutar lantarki a cikin kasuwannin mota ta Najeriya a shekara ta 2018, kuma za a fara shigo da sassan motocin domin hadawa a nan gida Najeriya a 2020.
Shugaban wannan kamfani, Malik Ado Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis din da ta gabata a ayayin tattaunawa da manema labarai a birnin Tarayya.
Ado Ibrahim ya bayyana cewa, kasashe da dama a fadin duniya sun kafa manufofin dakatar da motoci masu amfani da man fetur, inda kasar Indiya take da manufar shekarar 2030 da kuma Birtaniya, 2040.
Za a samar da motoci ma su amfani da wutar lantarki a Najeriya
Za a samar da motoci ma su amfani da wutar lantarki a Najeriya
Ya ce Najeriya da kasashen Afrika sun bukaci yin duba akan gaba don juyin juya halin na motoci ko kuma su shiga cikin hadarin zama kasashen da za su zama wajen zubar da motocin da wasu kasashen suka haramta amfani da su.

No comments