Cin hanci da rashawa: Hukumomin JAMB da NIMASA zasu fuskanci bincike

Share:

- Karkatar da kudaden da aka yi a hukumomin mai girman gaske ne in ji ministan kudi
- Ta ce dole tsaffin shuwagabannin hukumomin su bayyana don yin bayani
- Ministan ta ce za kuma a gudanar da bincike kan wasu hukumomin daban
Gwamnatin tarayya ta bada umurnin gudanar da bincike game da zargin yawaitan cin hanci da rashawa a hukumar jarabawa ta JAMB da hukumar Maritime ta NIMASA. An bayar da wannan umurni ne a jiya yayin wani tattaunawa da shugaban kasa ya jagoranta.
Cin Hanci da Rashawa: Hukumomin JAMB da NIMASA zasu fuskanci bincike
Ministan kudi, Kemi Adeosun ce ta bayyana hakan ga manema labarai a gidan Gwamnati. Ta ce satan da ake yi a Hukumomin guda biyu mai girman gaske ne. Sai dai bata bayyana hukumar da zata gudanar da binciken ba. Ta kuma kara da cewan za'a gudanar da bincike kan wasu hukumomin daban.

Ta ce a da JAMB bata samar da kudin da ya wuce naira miliyan 3 a shekara amma a yanzun ta samar da naira biliyan 5 da kuma wani karin naira biliyan 3 da ke shirin karuwa wanda gaba daya kudin da ta samar zai zama naira bilyan 8.
Ta ce haka shi ma NIMASA aka samu karin kudin mai yawan gaske fiye da yadda aka samu alhali hukumomin ba wai sun kara yawan kudin da suke karba bane. Don haka dole tsaffin shuwagabannin Hukumomin JAMB da NIMASA su zo suyi bayani.
A baya dai tsaffin shuwagabannin NIMASA irin su Raymond Omatsaye, Patrick Akpobologemi, da Mukaddashi Haruna Jauro sun gurfana gaban kotu bisa tuhuma na cin hanci da rashawa na makudan kudade. Shi kuwa tsohon shugaban JAMB Farfesa Dibu Ojerinde da aka kora a shekaran da ta gabata ya musanta cewan ba laifi ya yi aka kore shi ba.

No comments