Dandalin Kannywood: Har yanzu ban fidda ran dawowa harkar fim ba - Zainab Indomie

Share:
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa tana sa ran zata dawo harkar fim gadan-gadan ta kuma yi fice nan ba da dadewa ba.
Shaharraiyar jarumar wadda a yanzu haka tauraruwar ta ta riga ta dishe ta bayyana cewa tana nan tana murmurewa tana kuma kara kammala shire-shiren ta domin ta dawo da karfin ta ta kuma disashe taurarin wasu jaruman a harkar yanzu.
Dandalin Kannywood: Har yanzu ban fidda ran dawowa harkar fim ba - Zainab Indomie
Dandalin Kannywood: Har yanzu ban fidda ran dawowa harkar fim ba - Zainab Indomie

NAIJ.com dai ta samu cewa a kwanakin baya anyi ta rade-raden cewa jarumar tana fama da wata matsanaciyar rashin lafiya ne da kuma ta ke hana ta walwala da harkokin nata kamar yadda ta saba.
Haka ma dai a baya jarumar ta fito a kafafen sadarwar zamani inda tayi tofin Allah-tsine ta kuma sha alwashin yi wa duk wanda ya kara cewa tana fama da kanjamau Allah ya isa.

No comments