Rumbun Ilii: Yadda aka ƙirƙiri wani sabon manhajar Komfuta da yaren Hausa

Share:
An kaddamar da wata sabuwar manhajar na’aura mai kwakwalwa, wato Komfuta a Najeriya, wanda ya kunshi bayanai da dama da suka shafi rayuwar dan Adam, mai suna ‘Rumbun Ilimi.’
Shi dai wannan manhaja, Rumbun Ilimi, an yi shi ne don taimakawa wajen yin karatun Hausa a komfuta a saukake, walau ga dan makaranta, ko akasin haka, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Makirkirin wannan manhaja, Abubakar Muhammad Tsangarwa ya bayyana ma BBC Hausa cewa manhajar da aka yi tad a yaren Hausa na dauke da darussa daga bangarori daban daban, kuma shekaru 9 ya kwashe wajen kammala ta.
Rumbun Ilii: Yadda aka ƙirƙiri wani sabon manhajar Komfuta da yaren Hausa
Manhajar Komfuta da yaren Hausa
Abubakar yace baya da sha’awa, yayi wannan yunkuri ne domin zaburar da masana ilimin yaren Hausa dasu dage wajen yi ma harshen hidima, inda ya kara da cewa ya lura babu wani abu dake kunshe da yaren Hausa zalla a komfuta, hakan ta sanya shi fadawa kirkiro wannan manhaja.
Bugu da kari, manhajar na dauke da batutuwa akan abinci masu gina jiki, ilimin zamantakewa, kiwon lafiya da sauran su.
Daga karshe, makirkirin manhajar ya bada lambarsa kamar haka; 08039648244 ga masu bukatar manhajin, ko kuma a biyo shi a wahtsapp, ko a shafin yanar gizo na www.rumbunilimi.com, ko kuma a shafukan sadarwa zamani na Facebook da Twitter.

No comments