Shugaba Buhari zai yi jawabi a taron majalisar dinkin duniya, zai gana da shugaban kasar Amurka

Share:

- Ana sa ran shugabna kasa Muhammadu Buhari zai bar kasar Najeriya zuwa Amurka a ranar Talata, 19 ga watan Satumba
- Ana kyautata zaton Buhar zai gana da Donald Trump, shugaban kasan Amurka don yin jawabi a taron majalisan dinkin duniya.
- A cewar rahotanni, tuni Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje da mambobin fadar shugaban kasa sun isa kasar Amurka
Shugaba Muhammadu Buhari zai bar kasar Najeriya zuwa kasar Amurka a ranar Talata, 19 ga watan Satumba, don jawabi a taron majalisan dinkin duniya.
A cewar Sahara Reporters, ta samu labari daga gidan Najeriya dake New York cewa Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje na Najeriya da membobin fadar shugaban kasa suna a New York don tarban shugaba Buhari.
NAIJ.com ta tattaro cewa da farko, an shirya ganawa da Trump din ne tun makonni biyu da suka gabata amman aka daga saboda shugaban kasar na warwarewa ne wanda hakan ya hana shi tafiya a lokacin.

An fahimci cewa shugaba Buhari da tawagar Najeriya da zasu samu karbuwa a Millennium Plaza Hotel a First Avenue dake Manhattan yayin kwanaki biyar da zai yi a New York.

No comments