Za'a kaddamar da sababbin jiragen kasa a digar Abuja-Kaduna a Oktoba." — NRC

Share:
- Gudun jiragen ya kai 150km a awa daya
- Za su rage lokacin tafiya daga 2:45 zuwa 1:30
- An yanzu haka suna tashar jirgin kasa ta Idu a Abuja
In dai ba’a samu wata matsala ba, kamfanin jirgin kasa na Najeriya (NRC) zai kaddamar da sababbin jiragen kasa guda biyu da aka siyo don a fara amfani da su a kan digar Abuja-Kaduna a watan Oktoba.
"Za'a kaddamar da sababbin jiragen kasa a digar Abuja-Kaduna a Oktoba." — NRC
"Za'a kaddamar da sababbin jiragen kasa a digar Abuja-Kaduna a Oktoba." — NRC
Jiragen sun sun iso Najeriya a ranar 25 ga watan Yuli na 2017, sun kuma isa tashar Idu da ke Abuja a ranar 13 ga Agusta, 2017.
Kamfannin gine-gine na China (CCECC) ne suka dau nauyin safarar jiragen daga kasar waje har zuwa tashar Idun. Kuma a yanzu haka suna cikin shirin damkawa NRC su don su fara aiki da zarar sun gama gwaje-gwajen jiragen a hanyar.
Wadannan jiragen da aka siyo dama tun asali su ake niyyar amfani da su a hanyar jirgin kasan saboda sun fi gudu, a maimakon na yanzu da ake amfani da su. Na yanzu an sa su ne na wucin-gadi kafin aikin digar ya karasa.
Sababbin jiragen gudun su ya kai har zuwa 150km a awa daya, wanda zai rage lokacin tafiya Abuja-Kaduna daga awa 2 da minti 45 zuwa awa 1 da minti 30. Sannan kuma samuwar su zai kara lokutan tashin jirgi a kan hudun da ake yi a yanzu.

Wani mai magana da yawun NRC ya ce, “Za mu karbi jiragen daga hannun CCECC a cikin satinnan sannan zasu koya mana amfani da su kamar yadda suka yi mana na wadancan. Daga nan kuma ba zai dauki fiye da sati uku ba da mun gama gwaje-gwajen mu, zamu fara safarar mutane daga Abuja zuwa Kaduna.”

No comments