Messi zai je gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018

Share:
'Yan kasar dai sun yi ta murna da farin-ciki bayan da suka samu nasarar shiga gasar ta 2018.
Image'Yan kasar dai sun yi ta murna da farin-ciki bayan da suka samu nasarar shiga gasar ta 2018.
Cin kwallon da Lionel Messi ya yi sau uku ya sa Argentina ta samu kai wa gaci a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za a yi a Rasha.
Argentina ta samu nasarar ne bayan da suka doke Ecuador da ci 3-1 a Quito.
"Na shaida wa kungiyar cewa, ba Messi ne yake bukatar ya je gasar cin kofin duniya ba, gasar ce take bukatarsa," in ji kocin kungiyar.
Koci Jorge Sampaoli ya fadi haka ne bayan da Lionel Messi ya ci kwallayen da suka samu nasara a kan Ecuador, wanda ya tabbatar da Argentina ta samu nasarar kai wa shigar kofin duniya.
Messi ya ce, abun zai zama kamar al'amara idan aka ce Argentina ba ta samu shiga gasar da za ayi a Rasha ba, sai dai yanzu burinsa ya cika na samun damar zuwa gasar cin kofin duniya karo na 12 a jere.
'Yan kasar dai sun yi ta murna da farin-ciki bayan da suka samu nasarar shiga gasar ta 2018.

No comments