Abubuwa 19 suna sanya bushewar zuciya da kuma mutuwa babu imani?!!

Share:
ABUBUWA GUDA GOMA SHA-TARA (19) SUNA SANYA BUSHEWAR ZUCIYA DA KUMA MUTUWA BABU IMANI:

1. Rashin yarda da Qaddara.

2. Wulakantar da Sallolin Farilla.

3. Mu'amala da Kudin Ruwa (interest).

4. Cin dukiyar Al'ummar Musulmi ta hanyar haram.

5. Shan giya da sauran kayan maye.

6. Bijire ma Iyaye tare da wulakantar da zancensu.

7. Chanpi da tsafe-tsafe.

8. Zarcewa cikin Zina, Madigo, Luwadi. Ba tare da tuba ba.

9. Halasta duk wani abinda Allah ya haramta.

10. Rashin Girmama Abubuwa ko mutanen da Allah ya girmama su.

11. Sakin baki akan Manzon Allah, ko Ahalin gidansa ko Sahabbansa.

12. Kisan kai cikin ganganci.

13. Debe kauna daga samun rahamar Allah.

14. Qin karatun Alkur'ani da zikirin Allah..

15. Dogon buri tare da rashin tunanin lahira.

16. Cin amana, rashin tsayawa kan gaskiya, da kuma rashin cika alkawari.

17. Zaluntar marayu da Makobta da masu Qaramin Qarfi.

18. Rashin jin zafi idan an ta'ba hakkin Allah da Manzonsa.

19. Bayar da shaidar Zurr.

Ya Allah ka kiyaye mana Imaninmu zahiran wa batinan.

DAGA ZAUREN FIQHU (MARCH 11 2014).

No comments