AREWA HIP-HOP: Sanadiyyar Hip-hop Na Je Inda Ban Taba Tunani Ba – Lil Topeek

Share:

AREWA HIP-HOP: Sanadiyyar Hip-hop Na Je Inda Ban Taba Tunani Ba – Lil Topeek

1

    

Shaharerran mawakin Ingausa (Hiphop) Muhammad Topeek Yahaya wanda aka fi sani da Lil topeek wanda ya rera wakar MY BABY, ya kuma yi INA DA GAYU A LEGAS da wakar DARASI wanda sukayi tare da matashin mawakin hip hop S.K.D. A wannan tataunawa da ya yi wakilinmu Umar Muhsin Ciroma, yayi muhimman bayanai dangane da harkarsa ta waka, ya kuma ce yana yawan chanza suna ne saboda wasu dalilai, inda yake cewa kuma salon wakar hausa ta hiphop ya fi kowane kalar waka isar da sako, ga yadda hirar ta kasance:
Da farko dai za mu so mu san cikakken sunanka?
To asalin sunana shi ne Muhammad Topeek Yahaya.
Da wannan sunan kake amfani kana waka ko kana da wani sunan?
Farko dai da na fara waka na fara amfani ne da M. Boy, sannan daga baya na maidashi Young AB saboda wasu matsaloli da aka samu sai na yi tunanin na kuma canza wa na mai da shi lil-Topeek dama shi ne asalin sunana.
Me ya ja hankalinka ko ya baka sha’awa ka fara harkan waka?
A lokacin muna yara muna zama da abokaina muna saka wakokin Turanci Naija da na kasashen waje muna rerawa, muna kokarin juya su da harshen Hausa. Mun dade muna yin hakan sannan kawai water ana sai muka zauna muka rubuta waka sunanta ‘girls’ ita ce wakarmu na farko.
Kuma cikin ikon Allah wakar ta samu karbuwa a wajen Al-umma hakan ya bani karfin gwiwar cigaba da waka.
Kungiya ce lokacin kuka kirkira ko a’a kawai kun je kun yi ne kawai?
A’a lokacin kawai mun je Studio ne muka yi ta.
To yanzu aka yi kungiyar da kake aiki da su ne?
A’a gaskiya ba na amfani da wata kungiya a yanzu.
Kana sha’awar yin waka tare da wata kungiya ne ko kana yunkurin bude naka ne?
Gaskiya ni ba na yunkurin bude wata kungiya, sai dai mukan yi wakarmu kirari ni da abokina da mukan yi waka tare da “The Kingz of Arewa”.
Zuwa yanzu ka yi wakokin kamar nawa?
A gaskiya ba zan iya sanin adadinsu ba sai dai za su kai akalla guda 40 haka.
Ka taba yin album ne koko kawai kana yin sune daban daban?
Gaskiya ban taba yin album ba, amma yanzu nake shirye shiryen fitar da album dina.
Ya sunan album din?
Sunan album din “Kwalelanki”.
Wakoki nawa kasa a ciki?
Wakoki takwas ne.
Ko za ka iya kawo mana sunan su?
Eh, akwai, Kwalelanki, Kojo, wanda na saka har da Yaran North Side, Ni Da Ke, Bareera, Zo Mu Je, Lalala, wadda za mu yi tare da Emma Nyra; Oya Oya, sai Soyyaya, amma ina tunanin kara wasu a ciki.
Wani sako album din ke isar wa?
Akwai sakonni da dama kamar fadakarwa da nishadantarwa. Ka ga kamar ’Respect’ ita ma ina tunanin zan yi ta a album din, waka ce mai nuni akan kowa abashi martabarsa, yaro ko babba, a gida da waje, a kasa ko a cikin mota.
Wane irin kalubale ka fuskanta sadda ka fara waka?
Gaskiya na fuskanci kalubale da dama a lokacin da na fara waka wasu suna yi min kallon dan iska, amman haka bai sa na daina ba, sai kuma lokacin nakan rubuta wakoki da dama amma kudin shiga studio yakan zamar min matsala, yanzu dai Alhamdulillah.
A cikin wakokinka wane ka fiso, ko in ce ya fi birgeka?
Duk wakokina ina sonsu, sai dai yanzu ba zan iya cewa ga wacce nafi so ba, wacce al’umma suka fi so ita na fi so.
A’a ka zabi daya daga ciki wanda kai akan kanka kafi sauraran ta.
Eh to gaskiya za iya cewa nafi sauraran “Darasi”, wadda muka yi tare da wani abokina, kuma wakar tana birgeni ne saboda gaskiya ta bugu.
Kawo yanzu wani irin ci gaba ka samu a a harkar waka?
Gaskiya nasarori na same su da dama, don na samu mu karbuwa a wajen al’umma musamman na Kaduna, babban nasarar ma shi ne har yau masoya su kan kira ni su bani shawara, wasu ma ban san inda suke ba ta sanadiyyar waka ce na je inda ban yi tinaniba.
Wa kake koyi da shi a mawaka?
Gaskiya ni bana kwaikwayar wani, kullum kokari nake na ga na kirkiri abu nawa na kaina wanda zai burge al’umma.
To misali wane mawaki ka fi so ko ka fi son wakokinsa?
Gaskiya ba ni da wani mawaki da na fiso, sai dai inada mawakan da suke birgeni anan Nijeriya. Wakokin Wizkid suna birge ni, idan aka koma kasar waje kuma ina son Meekmill, Tyga, Young Thug.
Wace kalar mota ka fi so?
Gaskiya ina son Motoci irinsu Benz, Fomatable, Corolla S.
Wane irin abinci ka fi sha’awa?
Alale, Dan wake, sai Tuwo.
Wace shawara za ka bawa sauran mawaka ko masu son su fara?
Ina masu fatan alkhairi kuma mu dage mu hada kai guri daya don mu ma mu nuna Arewa ita ma ba a bar ta a baya ba. Kuma idan za ka yi waka ban da batsa, kuma wani abu da al’umma basu sani ba shi ne wakan hiphop yanzu a duniya ya fi, kowane kalar waka isar da sako. Dalilina kuwa shi ne duniyar baki daya na matasa ne kuma a wannan lokacin zai yi wuyan gaske kasarmu wayar matasa guda goma tara babu wakar hiphop a ciki, haka zalika ko zabe yau ka fito yau in matasa basu goya ma baya ba ba inda za ka je.
Daga karshe me za ka cewa masoyanka da abokan arziki?
Ina matukar gode wa Allah da ya hada ni da su, kuma ina kaunarsu kwarai da gaske, ina masu fatan alheri, kai har da ma wadanda ba sa sona ina masu fatan alheri, ka san an ce ra’ayi riga, sai wanda ka so za ka sa, don haka Allah hada kowa da rabonsa, Amin.

No comments