Ba A Bawa Salah Dama A Chelsea Ba -Hazard

Share:

    

 Abba Ibrahim Wada
Dan wasan gaban Chelsea Edin Hazard, dan asalin kasar Belgium ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ba ta ba wa tsohon dan wasan kungiyar dama ba, Muhammad Salah domin ya bayyana kansa.
Muhammad Salah, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ne a shekara ta 2014, sai dai wasanni 19 kawai ya buga a kungiyar, inda daga baya kungiyar ta tura dan wasan aro zuwa kungiyar Fiorantina ta kasar Italiya.
Bayan ya yi zaman aro na shekara guda, dan wasan ya sake aro kungiyar kwallon kafa ta AS.Roma ita ma ta kasar Italiya, inda nan ma ya yi shekara guda kafin daga baya kuma Roma ta biya Chelsea kudin dan wasan.
A watan Yulin da ya wuce ne Salah ya koma kungiyar kwallon kafa ta Liberpool daga Roma a kan kudi Fam miliyan 34, kuma a yanzu shi ne dan wasan da ya fi kowanne dan wasa zura kwallo a raga da kwallaye tara.
Hazard ya ce, Muhammad Salah babban dan wasa ne kuma kwararre, sai dai bai samu dama ba a Chelsea yadda ya kama, saboda wasu dalilai wanda bai san su ba.
Ya ci gaba da cewa, dawowarsa Ingila ta nuna wa duniya cewa babban dan wasa ne kuma yana da tunani da kokarin ganin ya zura kwallo a raga, sannan kuma ya taimakawa abokan wasansa domin ci-gaban kungiya.
A karshe Hazard ya ce, Salah na daya daga cikin manyan ‘yan wasan da Liberpool ke ji da su a halin yanzu, kuma ya yarda cewa yanzu ya zama abin tsoro idan ana wasa da Liberpool.
Chelsea da Liberpool za su fafata a ranar Asabar a wasan sati na 13, na gasar Firimiya da ake fafatawa a halin yanzu.

No comments