Basira: Wani matashi daga Arewa ya kera jirgin sama mai saukar angulu

Share:
Basira: Wani matashi daga Arewa ya kera jirgin sama mai saukar angulu

- Iyayen wannan yaron basu da halin biya masa kudin makaranta
- An bukaci gwamnati da al’umma sun tallafawa wannan yaron
Rahotanni sun nuna cewa wani yaro mai basira dan kabilar Igala a jihar Kogi ya kera jirgin sama mai saukar angulu ta hanyar yin amfani da kayan aiki wadanda ya samo asali daga nan gida.Kamar yadda NAIJ.com ke da labari , wani mai amfani da shafukan yanar gizo ta Facebook mai suna Audu Idris Iko-ojo, wanda ya wallafa hotunan a shafinsa, ya rubuta cewa;
“Wannan aikin hannun wani yaro dan kabilar Igala ne wanda ke zaune a okenya da ke gaban makarantar sakandare ta kwalejin kimiya, dan Mista sunday Emeje. Iyayen wannan yaron basu da halin biya masa kudin makaranta, amma yaron nada baiwa”.

“Gwamnatin jihar Kogi da na tarayya da kuma al’ummar Igala; menene zamu iya yi don motsa wannan yaro? idan ba mu yi wani abu yanzu ba, wani kasa zai iya kwace muna shi a nan gaba”.

Join our Facebook group now 

No comments