Dangote ya bada gudunmuwar Naira Miliyan 500 ga ‘yan kasuwan Kano

Share:

Dangote ya bada gudunmuwar Naira Miliyan 500 ga ‘yan kasuwan Kano


Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya bayar da tallafin zunzurutun kudi Naira miliyan 500 ga wadanda annobar gobara ta yi wa barna a kasuwannin Kano a shekarun baya
A taron tara kudin tallafin, wanda ya gudana karkashin jagorancin gwamnan Kano, an tara kudin da ya kai Naira Biliyan 1.5.
Dangote shi ne ya bada Naira miliyan 500, gwamnatin Jihar Kano ta bada Naira miliyan 500, sannan sauran wadanda suka bayar da gudunmuwa suka tara Naira miliyan 500.
Daraktan yada labaran gwamnan Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ne ya sanar da hakan a shafinsa na facebook.
A cewar Salihu Yakasai, tuni gwamnatin jihar ta tura na ta gudunmuwar asusuwan ajiya na musamman da aka bude domin tara kudin tallafin, sannan kuma ya ce za a tura na bangaren Dangote, wanda shugaban Gidauniyar Dangote, Mis Zouera Youssoufou ta gabatar. Sannan ya ce za a tabbatar da cewa an yi amfani da kudin kamar aka tsara.

Dangote ya bada gudunmuwar Naira Miliyan 500 ga ‘yan kasuwan Kano

No comments