FA'IDA DOMIN MAZAJE MASU AURE KADAI !!! Zauren fiqhu

Share:
FA'IDA DOMIN MAZAJE MASU AURE KADAI !!!
-----------------------------------
Tun ranar da na rubuto waccen fa'idar ta mata, kuke ta tambaya ta dangane da MAGANIN QARFIN MAZA.

To yau gani dauke da maganin da kuma shawarwari masu amfani INSHA ALLAHU.

Da farko dai babu abinda yake Qara tabbatar da mutunci da kuma soyayyar magidanci awajen iyalansa (matansa) kamar QARFIN GASARWA ALOKACIN SADUWA. Kuma babu abinda yake saurin zubar da mutum awajen matarsa kamar RASHIN KUZARI ALOKACIN SADUWA.

Sanin haka ne yasa kowanne namiji magidanci yake mutukar mai da hankalinsa akan duk abinda zai Qara masa karfin kuzari.

Cin abinci mai kyau mai gina jiki, mai Qara lafiyar jinin jikin mutum Yana daga cikin manyan abubuwan da suke Qarawa namiji Qarfin saduwa,

Irin wadannan abincin sun hada da 'ya'yan itatuwa, ganye da kayan lambu, Qwai dafaffe, madara, waken suya da sauransu.

Sannan motsa jiki shima jigo ne sosai. saboda wannan ne zaka ga yawancin mutanen da basu samun damar motsa jiki sunfi kowa fama da matsalar rashin Qarfin mazakuta.

Abu na uku kuma shine samun isashen hutu. shia jigo ne na samun Qarfin jiki gaba daya.

YAWAN RUWAN MANIYYI shima yana Qarawa namiji Qarfi da kuma kuzari da kuma dadewa alokacin jima'i.

ISASSHEN HUTUN da ka samu tun da rana, shi zai baka damar sake maimaita jima'in kamar sau uku ko hudu adare guda.

ABINCI MAI QARA LAFIYAR JIKI shi zai bawa jinin  jikinka damar hayayyafar isassun kwayoyin maniyyi.

GABATAR DA WASANNI KAFIN JIMA'I shima yana taiakawa wajen samun gamsuwa alokacin saduwa.

Manzon Allah (saww) ya hanamu saduwa da matayenmu ba tare da anyi wasanni da juna ba. gabatar da wasannin motsa sha'awa yakan Qara soyayya da annashuwa sosai.

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA RASHIN QARFIN MAZAKUTA:

Abubuwan suna da yawa. amma ga manya daga ciki.

1. BASUR DA MAJINAR CIKI: wannan shine babbar illar da yawancin matasanmu awannan zamanin suke fama dashi. 'kuma ba wani abune yake haifar dashi ba illa YAWAN SHAN KAYAN ZAQI DA MAIQO.

BASUR yana mutukar kashe karfin namiji harma mazakutar ta mutu gaba daya.

Duk lokacin daka samu maganin basur da majina mai kyau ingantacce kasha, to tabbas kai da kanka zaka ji chanji mai yawa. (watakil sai ka dade kana shimin albarka)

3 SHAQE CIKI DA ABINCI da kuma kwanciya kafin abincin ya narke. shima yana kawowa irin wannan matsalar. sai akiyaye arika cin abinci marar nauyi da daddare sannan adanyi nafilfili har abincin ya narke kafin afara aiki.

Sannan aguji batutuwan da zasu kawo bacin rai ko damuwa musaman ma da daddare.

Daga Qarshe nake bawa ma'aurata shawarar cewa babu laifi su rika chanza yanayin kwanciyarsu daga wani yanayin izuwa wani duk alokaci guda domin wannan ma yana janyowa Qarin dadewa da kuma gamsuwa alokacin saduwa.

SAI A PART 2 IN SHA ALLAH ZAN KAWO BAYANIN MAGUNGUNAN.

DAGA ZAUREN FIQHU (11-11-2017) Asalin rubutun anyishi tun 2014 ne.


No comments