FIFA Za Ta Dakatar Da Kasar Gambiya Daga Wasannin Kwallon Kafa

Share:

FIFA Za Ta Dakatar Da Kasar Gambiya Daga Wasannin Kwallon Kafa

5

    

Abba Ibrahim Wada
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ce dole ne Hukumar wasanni ta kasar Gambiya ta soke hukuncinta na dakatar da Shugabancin Hukumar kwallon kafa ta yi a ranar Litinin 27 ga watan nan na Nuwamba.
A wasikar da Fifa ta aika wa Hukumar, ta yi gargadin cewa, idan har ba a yi hakan ba nan da zuwa wa’adin da ta bayar ba, ko shakka babu za ta dauki kwakkwaran mataki wanda zai iya hana kasar ta gambiya shiga harkokin wasannin kwalllon kafa na duniya.
Har zuwa yanzu dai, Hukumar wasannin ta Gambiya ba ta ce komai ba game da wa’adin na Hukumar kwallon kafa ta duniyan.
A ranar 10 ga watan Nuwamba nan ne, Hukumar wasanni ta kasar ta dakatar da Shugabancin Hukumar kwallon kafar ta Gambiya a kan zargin aikata cin hanci da rashawa.
Hukumar ta ce ta dakatar da Shugabannin ne don samun damar gudanar da bincike a kan zargin da ake yi musu ba tare da sun yi katsalandan a cikin kwamitin binciken ba.
Idan dai har Fifa ta dakatar da kasar, to hakan zai hana kungiyoyinta shiga wasannin Nahiyar Afirka kuma ba wata tawagar wasan kasar da za ta shiga wata gasa da Fifa ta amince da ita.
Haka kuma, hukuncin zai iya hana zuwan alkalin wasa Papa Gassama, wanda shi ne ke samun lambar gwarzon lafiri na Afirka karo uku, gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi a Rasha.

No comments