Gareth Bale Zai Maye Gurbin Ozil A Arsenal

11
    
CHICAGO, IL - AUGUST 02: Gareth Bale #11 of Real Madrid reacts to a missed shot on goal during the MLS All-Star match between the MLS All-Stars and Real Madrid at the Soldier Field on August 02, 2017 in Chicago, IL. The match ended in a tie of 1 to 1. Real Madrid won the match on a 4 to 2 in penalty kicks. (Photo by Ira L. Black/Corbis via Getty Images)
Abba Ibrahim Wada
Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar kwallon kafar Arsenal ta fara tattaunawa da wakilin  dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Gareth Bale, don ganin ya koma kungiyar tasu.
Arsenal dai ta dade tana neman dan wasan mai kimanin shekaru 28 a duniya, wanda take da yakinin ganin zai taimaka mata wajen kara karfi a gasar Firimiya da kuma na zakarun Turai, sannan zai maye mata gurbin Mesut Ozil.
Yawan fama da jin ciwo da dan was an yake yi ya sa kungiyar ta yi sanyi da neman sa, kamar yadda aka sani wannan dan wasa dan asalin kasar Wales ne, wanda ya koma Madrid daga kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a kan kudi Fam milyan 83, a shekara ta 2013.
Bale ya buga wasanni goma ne kacal a wannan kakar tsakanin kungiyarsa Madrid da kasarsa ta Wales sakamakon yawan jin ciwo da ya rika samu, sannan  da alama dan wasan ya buga wasansa na karshe a wannan shekarar mai karewa bayan ya sake jin rauni a satin da ya gabata a filin daukar horo a kungiyar tasa ta Madrid.
Sai dai duk da yawan ciwon da dan wasan ya rika ji, hakan bai hana Arsene Wenger neman dan wasan ba, inda ta shirya tsaf don neman sa a kakar wasa mai zuwa.
Kazalika Madrid, ta yi wa dan wasan kudi a kan Fam miliyan 85 a kwanakin baya, duk da cewa dai a ‘yan kwanakin nan rahotanni sun bayyana cewa Madrid din ta rage farashin dan wasan zuwa Fam milyan 62.
Haka nan a kakar wasan da ta gabata dan wasan ya zura kwallaye goma sha biyu ne kadai a cikin wasanni 32 da ya bugawa Madrid kuma kasarsa Wales.