Inda ranka: Ma'aurata sun sayar da dan su na farko akan bashi a Najeriya

Share:

Inda ranka: Ma'aurata sun sayar da dan su na farko akan bashi a Najeriya

Runduna ta musamman ta 'yan sandan Najeriya a jihar Imo dake a kudu maso gabashin kasar nan sun samu nasarar cafke wasu ma'aurata Ifeanyi Anyanwu da matar sa Amarachi Ugorji bisa zargin laifin sata tare kuma da sayar da wani yaro mai shekara biyu a duniya kan kudi Naira dubu dari 500.

NAIJ.com dai ta samu cewa kafin wannan lamarin ya faru kuma, ma'auratan sun taba sayar da dan su na fari a bisa bashi zuwa ga wani mutum a garin Fatakwal babban birnin jahar Ribas a shekarun baya.
Da yake karin haske kan lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar rundunar 'yan sandan jihar SP Andrew Enwerem ya tabbatar da faruwar hakan yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a farfajiyar rundunar a garin Oweri.

No comments