kannywood» "Ni ce jahila? Na barku da Allah" Hira da Ummah Shehu

Share:

A kwanakin baya, jaruma Ummah Shehu ta zama wata babban topic da aka ta tattaunawa sakamakon wani faifan video da ya yadu a dukkan kafofi na sadarwa.

A wata tattauna da jarumar, ta bayyana yadda abun ya bata mamaki domin a cewar ta, abun da tayi cikin wasa da raha amma sai gashi mutane masu neman kurakuren wasu sun dauka sun ta yadawa.


Jarumar ta bayyana wannan kokari na su a mamakin abun haushi da takaici, kuma abun ya mata ciwo a mata gorin ilmin addini duk da yaqinin da take da shi na cewa ita gogaggiya ce a wannan fannin, wannan na ma daga cikin dalilan da suka sa ta zabi harkan fim domin bada tata gudunmawa a fadakar da jama'a.


Daga karshe ta bayyana dukkan wata matsala ko tuntube a rayuwa a matsayin kaddama kuma mutum ba zai ci gaba ba ba tare da yana samun irin wadannan jarrabobin ba, kaman yadda bahaushe yake cewa "hassada ga mai rabo taki"

No comments