kannywood» Wata sabuwa! Jarumi Adam Zango zai saka wando daya da masu masa zargin karya

Share:

Jarumi yace duk macen dake zargin sa da yin lalata da ita kafin ya saka ta a fim ta fito fili ta bayyana ma duniya

Fitaccen jarumin fina-finan hausa kuma mawakin hausa Adam A.Zango ya bayyana da abun dake ci masa tuwo a zuciyar sa kuma ya shirya damawa da duk wanda ke neman lalata masa suna.

Jarumin 'Gwaska' ya fitar da fushin sa a shafin sa na kafar sadarwa ta instagram inda ya kira kansa da damisa kuma wanda ya nemi shi da fada ba ya neman zaman lafiya.

"Kayi kuskure daka tada damisa dake bacci. Ka dau alkawarin ganin na fadi daga daukakan da na samu, wannan ya nuna cewa kuna karkashi na.... .don haka mu zuba mu gani shege ka fasa dani daku."

 ya rubuta.
Kana a wani sako da ya kara fitar, shaharren jarumin ya bukaci mata dake masa zargi na yin lalata da mace kafin ya bata damar fitowa a fim dinshi ta fito fili ta bayyana ma jama'a.

"DUK WADDA DA TACE SAINA NEMETA KAFIN IN SAKATA A FILM TA FITO GIDAN TV KO REDIO STATION TA FADAWA DUNIYA. IDAN KUMA TA RUFA MIN ASIRI ALLAH YA TONA MATA NATA ASIRIN."

Tun ba yau ba ake zargin yan wasan kannywood da yin lalata da mata kuma sun fito fili wajen musanta wannan zargin da ake masu.

Join  our facebook group 
https://m.facebook.com/profile.php?id=129667237690008&ref=content_filter

No comments