Za’a Binciki Batan Dala Biliyan 60 A Babban Bankin Nijeriya

Share:

Za’a Binciki Batan Dala Biliyan 60 A Babban Bankin Nijeriya


Kwamitin sauraren korafe-korafe na majalisar wakillai, ya ce zai binciki badakalar zargin batan wasu makudan kudaden da suka kai Dala Biliyan 60 na riba da harajin mai da ake saidawa a asusun gwamnati na babban bankin Nijeriya.
Shugaban Kwamitin Uzoma Nkem-Abonta ya bayyana haka a Abuja, biyo bayan kin mutunta goron gayyatar da babban bankin Nijeriya yayi na halartar zaman da suka yi.
Uzoma, ya ce za su fara binciken ne da taron neman jin ra’ayin jama’a game da abin da za su shirya su kuma yi nan ba da jimawa ba.
Badakalar kudin dai ta samo asali ne daga wata takardar koke da wani Mista Fidelis Uzonwani ya rubuta wa kwamitin, inda ya tsegunta cewa daga shekara ta 2004 zuwa ta 2016, sama da Dala Biliyan 60 ce ta bace daga asusun babban bankin Nijeriya.

No comments