Zango Ya Nemi Afuwar Masoya Kan Zazzafar Wasikarsa


149
    
A wata budaddiyar wasika da Adam Zango ya rubuta ya sanya a shafinsa na Instagram, ya koka da irin yadda ake ta yi masa zargi kan abubuwan da bai ji ba, bai gani ba. A wasikar ta Zango, ya bayyana cewa,  idan har ba a daina yi masa irin wannan kazafi ba, zai fara bayyana sunayen masu yi masa wannan zargi.
Haka zalika, shafin yada labaru ta intanet na Premium Times Hausa ya ruwaito cewa Jarumin ya kalubalanci duk wanda ke da wata kwakkwarar hujja cewa ya aikata abin da ake zargin nasa da shi, kada ya rufa masa asiri ya fito ya fada wa duniya. Ga dai yadda zubin wasikar tasa ta kasance kamar haka:

Budaddiyar  Wasika Ga Makiyana
“Ni ba dan daudu ba ne kuma ni ba dan maula ba  ne. Kazalika, ni ba mushiriki ba ne, ba ni da Malami ko Matsafi.
“Da Allah kadai na dogara, idan kuma akwai Malamin da ya ce na taba zuwa wajensa ko kuma wanda ya taba ba ni kudi kyauta, ba tare da na yi masa aikin komai ba, to don girman Allah kada ya rufa min asiri; tun daga kan ‘yan Siyasa, Sarakuna, Gwamnati ko masu kudi ko kuma ‘yan mata. Duk abin da da na mallaka a rayuwata, gumina ne ya ba ni; ba wani dan Adam ba, kama daga kan motar hawa, gida ko fili.
“Don haka, babu wani wanda ya isa ya sa ni in yi abin da ban yi niyyar yi ba, tunda babu wanda ya taya ni kare mutuncin daukakata.
“Haka zalika, ta hanya daya tak za ku iya dakatar da daukakata, hanyar kuwa ita ce dakatar da numfashina, sai dai kuma kash! Ba a hannunku yake ba, haba, ku yi ta yawo da ni kuna bata min suna don kawai Allah Ya fifita ni a kanku.
“Kun ce ni arne, kun ce da ni dan neman maza, fasiki kuma  mai girman kai, amma duk da haka masoyana ba su guje ni ba, ba su daina sayen fina-finai da wakokina ba. Haba don Allah mai na yi muku? Duk wanda na taimakawa a rayuwata sai ya dawo yana yaka ta. To yanzu na kai bango, duk wanda ya ce da ni kule, zan ce da shi cas.
“Billahillazi la’ila ha illahuwa, duk wanda ya kara taba ni, sai na tona masa asiri. Sannan duk wanda ya rufa min asiri a kan abubuwan da na lissafa, Allah Ya tona masa nasa asirin. Ban kira sunan kowa ba a yanzu, amma nan gaba zan kira sunan duk wanda ya sake bata min suna. Dalili kuwa, ina da ‘ya’ya, ya zama dole na fara kare mutuncina da martabata tun kafin abun ya fara shafar ‘ya’yan nawa kai tsaye, tunda Allah ne kadai Ya san gawar fari. Sannan zan ja zare da mabiyana na Kannywood, don a haka ne kadai za a iya bambance tsakanin aya da tsakuwa. Amma don Allah masoyana ku gafarce ni a kan Abubuwan da na rubuta, an kai ni makura ne,” in ji Zango.
Har yanzu dai ba a gano takamaimen wadanda Zango ya rubuta wa wasikar maigauni ba, amma dai masu iya magana sun ce