Ba za mu yarda a saba wa Allah a otel dinmu ba – Kungiyar Izala

Share:

Ba za mu yarda a saba wa Allah a otel dinmu ba – Kungiyar Izala

- Shugaban kungiyar Izala Abdullahi Bala Lau ya ce bukata ce yasa suka gina masaukin baki a Abuja

- Malam Bala Lau ya ce a matsayin su na kungiyar Addini baza su bari a sabawa Allah a Otel din da su gina ba
Shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce bukata ce ta sa kungiyar ta gina katafaren Otel a Abuja.
Malamin ya ce sun gina Otel din ne dan samar wa mallaman su masauki a birnin Abuja.
Abdullahi Bala Lau yace, yakamata a matsayin na mallamai addini su samu kebabben wajen saukar da baki da aka tsara shi bisa ka’idojin addinin Musulunci.

Kuma a matsayin su na kungiyar Addini ba za su bari ana sabawa Allah a ciki wajen masaukin bakin da suka gina ba.

No comments