Babbar kotun tarayya ta yi wurgi da bukatar Maryam Sanda, an sake garƙame ta Kurkuku

Share:

A cigaba da sauraron karar da rundunar Yansanda ta shiga da wata mata data kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka, Maryam Sanda, a yau ma babbar kotun tarayya dake Jabi ta yi zaman sauraron karar.

Daily Trust ta ruwaito a zaman na yau, kotun tayi watsi da bukatar bada belin Maryam Sanda da lauyan ta ya shigar a gaban Alkali, sa’annan kotun ta kara bada umarnin a tasa keyarta zuwa gidan kaso.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito rundunar Yansandan Najeriya ta shigar da karar Maryam Sanda akan tuhume tuhume guda biyu da suka danganci kisan mijinta, Bilyaminu da ake zargin ta yi.
Ita ma mahaifiyar Maryam Sanda, Hajiya Maimuna Aliyu Sanda tana fuskantar tuhume tuhume a gaban wata kotu kan zargin ta da aikata babakere, cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudaden al’umma a bankin Aso Savings.

Idan za’a tuna, an bayyana marigayi Bilyaminu a matsayin yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Halliru Bello, kuma ya mutu ne sakamakon wuka da matarsa ta caccaka masa biyo bayan ganin wasikar wata budurwa a wayarsa.

No comments