Dalilin da yasa nafi karkata wajen yiwa mata wa'azi - Sheikh Kabiru Gombe

Share:

Dalilin da yasa nafi karkata wajen yiwa mata wa'azi - Sheikh Kabiru Gombe

Sakataren kungiyar nan ta wa'azi a Najeriya dama wasu sannan kasashen Afirika ta Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) na kasa Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya bayyana a cikin wata fira da yayi da majiyar mu dalilin da yasa wa'azin sa yafi karkata akan mata.

Shahararren Malamin islaman dai ya bayyana cewa ya fuskanci cewa an bar iyayen namu matan ne a baya musamman ma ta fuskar wa'azi da sauran al'amurran addinin musulunci baki daya.

NAIJ.com dai ta samu cewa haka zalika malimin yayi ikirarin cewa tabbas wa'azantar da 'ya'ya matan yafi na mazan muhimmanci domin suma tamkar wata makaranta ce sukutum a cikin gidajen su da kuma 'ya'yan da suka haifa.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa Shehunnan malaman na Izala da suka hada da Sheikh Bala Lau da kuma Kabiru Gombe sun lula zuwa kasar Ingila a Birnin Landan a cikin satin da ya gabata domin gabatar da wata lacca inda kuma hotunan malaman ya watsu sosai musamman ma a kafafen sadarwar zamani sanye da tufafin Turawa.

No comments