Dandalin Kannywood: Har yanzu miji nagari nike nema - Inji Fati Muhammad

Share:

Shahararriyar fuskar nan ta masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Fati Muhammad ta bayyana cewa ita har yanzu tana neman miji nagari ne shi yasa ta kasa yin aure.

Jarumar ta yi wannan bayanin ne a cikin wat fira da tayi da mujallar fim inda ta bayyana cewa tabbas dukkan mace ta so tayi aure ta kuma zauna a dakin mijin ta to amma hakan na samuwa ne kawai idan har ta samu mijin nagari da zai mutun ta ta.


NAIJ.com dai ta samu cewa jarumar ta kara da cewa takan ji matukar dadi idan har taji mutane na cewa tayi aure don kuwa a cewar ta, ta san dole sai mai son ka ne zai yi maka wannan fatar.
Haka nan kuma sai ta roki masoyan ta da su daure su cigaba da sa ta a addu'a har Allah ya cika mata burin ta ta samu wanda zai aureta ya kuma rike ta amana da mutunci domin a cewar ta aure shine cikar darajar 'ya mace.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumar a kwanan baya ta bayyana cewa ba zata taba iya sake auren dan fim ba domin a cewar tayi bata ji da dadi ba.

No comments