Gasar cin kofin Duniya: Ina fargabar haduwa da Najeriya - Inji Lionel Messi

Share:

- Messi ya bayyana cewa tawagar Najeriya cike take da gogaggun 'yan wasa

- Shahararren dan wasan ya kuma bayyana cewa 'yan wasan Najeriya sun iya zura kwallaye
- Haka zalika ya ce mai horas da su shima gogaggen gaske ne
Shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan asalin kasar Argentina da kuma yake bugawa kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Sifen ya bayyana shakkun sa game da yadda karawar su zata kasance da kasar Najeriya a gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 da za'a gudanar a kasar Rasha.
Ita dai kasar ta Argentina an kasafta ne ne a rukunin 'D' tare da Najeriya, Iceland da kuma Croatia a gasar da za'a fara cikin watan Yuni na shekar ta 2018 mai kamawa.

NAIJ.com dai ta samu cewa shahararren dan wasan ya bayyana shakkun nasa ne a yayin wata fira da yayi da gidan Talabijin na kasar tasu inda ya bayyana tawagar kasar Najeriya din a matsayin wadda take da gogaggun 'yan wasan da suka iya taka leda a kungiyoyin su daban-daban da suke.

Amma kuma a cewar sa, tawagar kungiyar 'yan kwallon ta Najeriya tana da nakasu waje guda inda sukan bar fili da dama ga abokan hamayyar su su samu sararin yin wasa sosai don haka za su iya fitar da ita cikin sauki.

No comments