Google Sun Kaddamar Da Application Mai Rage Shan Data

Share:
Daga  Bakir Muhammad
 Kamfanin Google sun kaddamar da wani afilikeshan mai suna Datally, wanda suka yi shi musamman don manyan wayoyin hannu na Android, wanda zai takaita da rage yawan shan data da wayoyin suke yi.
Datally zai yi aikin akan duk wayoyin hannu na Android da suke da tsarin android 5.0 zuwa sama, ana iya samun shi a Google Play Store domin saukewa.
Misis Juliet Chiazor Darektar kamfanin Google a Nijeriya tace, ‘a cikin shekaru da suka gabata tawagar masu bincikenmu suna ta kokarin samar da hanyoyin saukakewa ga kasashe masu tasowa a harkar intanet kamar Nijeriya, kaddamar da Datally a kasuwar manyan wayoyi a Nijeriya zai matukar taimakawa masu amfani da manyan wayoyin wajen rage cin data, Google sun yi gwajin afilikeshan din Datally ne a kasar Filifins a cikin shekarar nan ta 2017, kuma sakamakon gwajin shine ya tabbatar da yanayin yadda afilikeshan din zai kasance, bincike ya tabbatar da wadanda suka yi amfani da Datally sun iya rage cin data da kashi 30 cikin dari.’
An kaddamar da Datally ne domin rage amfani da data a manyan wayoyin android a fadin duniya musamman a Nijeriya, inda ake korafi akan yawan datar da ake konawa, a wani bincike da aka gudanar a fadin duniya don gano yawan datar da masu amfani da manyan wayoyin hannu suke konawa, an gano da yawan masu amfani da manyan wayoyin suna damuwa da rashin data a wayoyinsu na hannu, musamman masu matsakaitan shekaru da suke amfani da wayoyin.
‘Ba wai kawai suna damuwa da karancin datar bane, A’a suna kasa gane ina datar su take shiga, kuma basu san ina take zuwa ba, sannan basa tunanin takaita amfani da data ga afilikeshan da suke yawan amfani da shi, inji Wojcicki.
Afilikeshan din zai kara taimakawa masu amfani da wayoyin wajen rage cin datar da manyan wayoyinsu suke yi ta hanyar amfani da abubuwa hudu.
Na farko shine Data Saber: afilikeshan da dama na amfani da data ko waya ba a bude su ba domin su dinga sabunta bayanai a ko da yaushe, wannan fasahar ta Data Saber zata bai wa masu amfani da wayoyi damar kayyade cin datar ko wanni afilikeshan a kashin kansa, don haka ba kowanne afilikeshan bane zai dinga shan data ko yaushe.
Data Saber Bubble: in aka bude afilikeshan din Data saber, akwai wani balo balo da zai bude wanda yake nuna mutum ya shiga wani afilikeshan, da zarar wannan afilikeshan din ya yi amfani da data, to balo balon zai nuna yawan datar, don haka zai zama da sauki a iya rufe shan datar, abun dai tamkar mitar auna gudun mota ne, amma mai auna cin data.
Personalized alerts: Datally zai ankarar da mai amfani da waya da zarar wani afilikeshan ya fara cinye data, sannan yana bada damar gane yawan datar da aka ci a kullum, duk sati, ko duk wata.
Wi-Fi finder: akwai lokuta da masu amfani da wayoyin hannu za su so yin amfani da data mai yawa sosai, misali suna so su kalli bidiyoyi masu nauyi sosai, akwai intanet wacce ake sakawa a guraren taruwar jama’a don amfanin kowa da kowa (Wi-Fi), Datally yana iya gano wanne ne yafi kusa, yafi karfi sabis, amfani da wannan irin intanet din yana da matukar sauki.

No comments