Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 a mulki

Share:

- Gwamnatin tarayya na lissafa jerin aiyukan da ta kammala a yayin da muke bankwana da shekarar 2017

- Ma'aikatar aiyuka, lantarki, da gidaje ta fara sakin jerin aiyukan da ta yi a fadin Najeriya
- Ma'aikatar ta ce bayan gina sabbin hanyoyi, ta gyara wasu hanyoyin da tsayin su ya kai kilomita 430
Ma'aikatar aiyuka, lantarki, da gidaje ta ce ta gina hanyoyin mota da nisan su ya kai kilomita 366 tare da gyaran wasu hanyoyin da tsawon su ya kai kilomita 430, a fadin Najeriya. Hakazalika ma'aikatar ta ce ta kammala ginin gadoji 24, tare da gyara wasu gadojin 19.


Ga jerin hanyoyin da gadojin da aka gina ko aka gyara kamar haka:
1. An kirkira tare da kammala gina sabbin hanyoyi masu nisan kilomita 366 cikin shekaru 2
2 . Anyi gyaran wasu hanyoyin da tsayin su ya kai kilomita 430
3. An gina sabbin gadoji guda 24
4 . An gyara wasu gadojin 19 da tsawon su ya kai mita 3,488
5 . An gina kwalbati da tsawon su ya kai 260,461
6 . An gina magudanan ruwa masu tsawon mita 260,461
7. Akwai hanyoyi masu nisan kilomita 1,221 da ake saka ran fara aikin su kowanne lokaci.
Ma'aikatar ta ce aiyukan da ta kirkira sun samar da aikin yi ga mutane 17,749 a kowanne mataki.
Saidai duk da wadannan aiyuka da ma'aikatar ta ce ta shimfida, 'yan Najeriya na cigaba da korafi a kan rashin ingantattun hanyoyi dake jawo yawaitar hadurra tare da asarar rayuka da dukiyoyi.

No comments