Injiniyoyi 2 yan Najeriya sun kera nau’arar janareta da baya amfani da man fetur ko gas

Share:

- Injiniyoyi biyu daga jihar Anambara sun kera janareta mara amfani da man fetur gas

- karfen janaretan zai iya ba wa fanka talabajin da karamin frij wutan lantarki na tsawon sa’o’I 48
- Janaretan yana da sauki amfani kuma bai da tsada inji Ezeilegbunam
Wasu Injiniyoyi biyu yan Najeriya daga jihar Anambara Gabriel Obinna da Moses Ezeilegbunam sun kera na’uarar janareta mara amfani da man fetur da gas.
Injiniyoyin sun ce, karfen janaretan zai iya ba wa fanka, talabajin da karamin frij wutan lantarki na tsawon sa’o’I 48.
Sunce idan suka samu kudi za su iya kara karafin wutar lantarkin janaretan, ta inda zaiy iya daukan nauyin manyan na’urori.


Ezeilegbunam yace yan Najeriya suna matukar bukatar irin wannan janareta a yanzu saboda rashin ingantaccen wutar lanatarki a kasar. kuma yana da saukin amfani.

Saboda rashin wutar lanatarki yana hana kasa cigaba da janyo koma bayan tattalin arziki.
Duk dan Najeriya, mai kudi ko talaka yana fusknatar matsalar rashin wutan lantarki.
Kuma ko mutum ya saya janareta, yana bukatar sayan man fetur ko gas, wanda farashin a kullum cikin karuwa yake.

No comments