Kannywood sun yi fim din Maryam Sanda da Bilyaminu marigayi

Share:

Fostar fim din, ta nuna wata mata da jajayen kaya ta caka wa wani saurayi wuka lokacin yayi sujjada a sallah. Wasu na ganin yin fim din bai dace ba musamman ganin yadda batun ke gaban kotu. Wasu kuma na ganin ma tunda wani ya rasu, bai kamata wasu su ci kudi da hakan ta hanyar fim ba.


Fim din ta kashe shi, fim ne da Jamilu Ahmad Yakasai ya shirya, kuma har sun fara sayar dashi a kasuwa.
A labarin dai, kamar yadda aka ji a gaske, wata mata ce tsananin kishi ya sanya ta kashe mijinta yana cikin sallah, saboda zai karo mata kishiya.
Masu hada fim din na fata ne su fadakar da jama'a kan mugun kishi da abin da zai tarwatsa ma mutum rayuwa

A waje daya kuma, wasu na gani tunda batun yana kotu, bai kamata ayi fim din ba, ko ma kuma cewa wani ya rasa ransa a gaske, bai kamata ayi ffim a ci riba dashi ba

No comments