Shin menene bitcoin???

Share:
Shin minene bitcoin??

Bitcoin wani tsarin kudi ne da ake amfani da shi a intanet kadai, kuma ya na amfani a duk 
duniya ta hanya bai daya, kuma babu wani banki guda daya da yake kula da wannan nau’in kudin, wani masanin fasaha mai suna Satoshi Nakamoto ne ya kirkiro fasahar Bitcoin a shekarar 2009, kuma masu tahammulli da nau’in kudin sun a yi a tsakanin su ba tare da wani mutum na uku ba wanda zai lura da tahammulin tsarin sakar sama na intanet ne kawai ke kulla tahamullin.
Ana yin amfani da kudin Bitcoin wajen musanyar kudade a sahar intanet, ana iya siyan hajoji ma, a shekarar 2015 kadai ‘yan kasuwa kimanin 100,000 ne suka yi mu’amala da kudin Bitcoin, ana iya amfani da kudin na Bitcoin domin zuba hannun jari a wasu kamfanoni, a wani bincike da jami’ar Cambridge ta gudanar a shekarar 2017 ta gano akwai akalla kusan mutum sama da miliyan biyar da suke amfani da kudin na Bitcoin.

Ta Ya Ya Wannan Na’uin Kudin Yake Aiki?
Wannan it ace tambayar da kowa yake  yi in ya ji maganar wannan nau’in kudin, kamar dai yadda wadanda su ka san yadda ake kulla cinikayya ta sahar intanet, mutum zai siya abunda yake so sai ya biya ta akant din sa a shagonnan da su ke sahar intanet (Online Stores) to haka shima Bitcoin ake cinikayya da shi akwai shagonnan sahar intanet da suke yarda da cinikayya da nau’in kudin na Bitcoin, ta yadda mutum in ya ga abun da ya ke sha’awar siya a shagonann sahar intanet da suke karbar nau’in kudin sai kawai ya shiga bayanen jikar ajiyar kudin shi na Bitcoin (Wallets) a take shagon sahar intanet za su cire kudin su daidai da cinikayyar da ya yi.

Ya Ake Samun Kudin To?
Akwai hanyoyi da yawa na samun wannan nau’in kudin, misali na farko shine ana siya ta sahar intanet, akwai shafukka na sahar intanet da suke siyar da nau’in kudin, mutum zai shiga shafin sai ya zabi yawan Bitcoin da yake bukata sai a cire kudi a take daga akant din shin a banki, a take kuma za’a sa mishi wannan adadin na Bitcoin a jikar ajiyarshi ta intanet wato (Wallet), ana iya samun Bitcoin a shafukkan wasanni na intanet (Online games) in mutum ya buga wasa ya yi bijinta sai a bashi kyautar Bitcoin in da zai daura bayanin jikar ajiyarshi a take Bitcoin zai shiga jikar tashi, da kuma wasu hanyoyin amma wadannan su suka fi shahara.

Ya Yanayin Darajar Kudin Yake?
kudin ya na da daraja sosan gaske, kudin ya ninka zinare daraja sau bakwai, ya ninka dalar Amurka daraja sau goma sha takwas, ma su buga caca a sahar intanet ne su ke sa darajar kudin yak e hauhawa ko wanne lokaci, an fi amfani da shi a kasashen Amurka da Kanada da kusan duk kasashen turai, da kasar Sin da kasar Jafan.

Shin Ba Matsalar Tsaro Wajen Amfani Da Kudin?
Shi dai ba kamar kudin takarda bane, babu yadda za ayi barayi su sace shi ko masu kutse su kutsa su gano lambar katin banki su yi sata a akant din ajiya, shi abu ne da ya ke amfani da adireshin mutum wanda shi kadai ya san abun shi, abu daya aka fi tsoro wajen amfani da kudin, samun mazambata da ka iya siyar wa mutum kayan bogi sai a tura musu wannan kudin, ko kuma su siyar wa mutum Bitcoin ya biya su da kudin takarda amma su ki tura mishi Bitcoin din cikin jikar ajiyar shi ta intanet.
A yanzu ana kara samun masu amfani da kudin Bitcoin misali kamfanin hada-hadar kudi na intanet wato PayPal wanda yak e kasar Amurka ya na amsar kudin na bitcoin, haka kamfanin Microsoft ma mai kera wayoyi da kwamfutoci da manhajjojin kwamfuta (Softwares) da kamfanin Dell shi mai kera kwamfuta da wani kamfani mai suna Newegg.

Menene Tsarin Manhajjar Android (Android system)?
Android kamar yadda kowa ya sani wata nau’in tsarin manhajjar waya ce da ke kishiyantar manhajjar iOS da ta Blackberry, kamfanin Google ne suka kirkire wannan tsarin manhajjar ta Android, kuma ta na amfani da wata fasaha ne mai suna Linud Kernel wacce aka yi ta musamman don manyan wayoyin hannu wanda ba sa amfani da madannai, amma an fadada fasahar yanzu akwai talbijan, da motar hawa, da agogon hannu da kyamara duk ma su amfani da tsarin Android.
A shekarar 2005 aka kammala tsarin manhajjar ta Android amma ba’a kaddamar da shi ba sai a shekarar 2007, an kaddamar ne tare da manhajjar da ta dace da ta tsarin Android (Applications) da kuma bangarorin da su ma za su dace da tsarin manhajjar (Hardware) misali lasifika, da wajen Magana (Microphone) ga gilishin gaban waya (Touchscreen) da sauran su masu yawa, a shekarar 2008 aka kaddamar da wayar hannu mai amfani da tsarin Android ta farko.
Andy Rubin da Rich Miner ne suka kirkiro wannan tsarin manhajjar a Palo Alto da ke garin California na kasar Amurka, sun kirkiro wannan tsarin manhajjar ne domin ciyar da amfani da wayoyin hannu gaba, tsari ne da zai taimaka matuka wajen sannin ainihin inda wanda yake amfani da wayar yake, da kuma  sannin me ya fi bukata,a lokacin babu manyan wayoyi sai wadanda suke amfani da tsarin manhajjar Symbian da Microsoft window kadai, su kuma basa wadatar ba wajen wasu abubuwan.
Wayoyin da suka fara fitowa da wannan tsarin manhajjar android sune HTC kamfanin kasar Taiwan, Motorola da Samsung, wayoyin da suka fitowa da tsarin manhajjar mafi ywansu sunyi kama da wayoyin Blackberry wato basu da gilashin tabawa (Touchscreen) sai madannai kawai, amma fitowar wayar iPhone mai amfani da tsarin manhajjar iOS ta farko wacce ba ta da madannai ya sa aka canza yanayin Android daga wacce take da madannai zuwa wacce ba ta da madannai sai gilashin tabawa kawai.
Wayoyi da suka fara fitowa suna da tsarin manhajja nau’i daban daban, misali akwai “Cupcake” da “Donut” da “Éclair” da kuma “Froyo”, a shekarar 2013 yayin kaddamar da tsarin manhajja nau’in “KitKat” kamfanin ya sanar da tsarin sanya suna na nau’in tsarin manhajojin wayar, y ace daga lokacin za su dinga sama mu su sunaye irin sunayen abubuwan kwalam da makwalashe (Desserts), sanadiyar jin dadi da wayoyin suke kawo ma rayuwar ma su amfani da su.
Wayoyin ma su amfani da tsarin manhajjar Android sun fi sauran kishiyoyin su saukin amfani, sunfi arha ma a kasuwa, sannan manhajjojin (Apps) da masu amfani da wayoyin su ke bukatar amfani da su suna da saukin samuwa, a na iya samun su a kantin manhajjoji na “Google Store” da yak e zuwa a kan ko wacce wayar Android, da yake wayoyin da batir su ke amfani, duk lokacin da ba a amfani da wata manhajja to wayar da kan ta za ta kulle wannan manhajjar saboda ta rage shan batir, sannan kayayakin wayar Android suna da saukin mu’amala, ta yadda ba za a sha wahala ba wajen gyara su in sun samu matsala.
A halin yanzu duk da matsalar tsaro da masana suka ce wayoyin na android suke da shi mafi yawan mutanen duniya da suke amfani da manyan wayoyin hannu da Android suke amfani, akwai kamfanoni sama da hamsin da suke kera wayoyin android, sannan ko wanne kamfani ya na da nau’ikan wayoyin akalla sama da goma, sannan akwai kamfanoni da ba su tsaya a wayoyin hannu ba kawai, akwai Talbijan mai dauke da tsarin manhajjar android, akwai agogon hannu ma, ga kuma motoci masu sarrafa kansu duk suna dauke da tsarin manhajjar ta Android.

No comments