- Shugabannin kungiyar Izala sun dawo Najeriya daga kasar Burtaniya

Share:
- Jirgin da ya dauko su ya saka ne a babban birnin tarayya Abuja
- An hango babban sakataren kungiyar Sheikh Kabir Haruna Gombe tare da shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau cikin fara’a
A safiyar yau Talata, 12 ga watan Disamba jirgin day a dauko manyan malaman kungiyar Izala daga kasar Burtaniya ya sauka a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe.
Jirgin wanda yake dauke da Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da Sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe, ya sauka a babban birnin tarayya Abuja.

An hango babban sakataren kungiyar Sheikh Kabir Haruna Gombe tare da shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau sun sauko cikin fara'a suna ta fadin "Alhamdulillah" wanda Alamu ke nuna sun samu gagarumar nasara a bulaguron da sukayi na aikin Da'awa a kasashen Turai.

No comments