Waiwaye: Muhimman abubuwa da suka faru a 2017 a Najeriya

Share:

Waiwayen NAIJ.COM na yau shine muhimman abubuwa da suka faru a 2017. A 2017, anyi kokarin ruguje Najeriya, kasar ta kusa rasa shugabanta ga rashin Lafiya, jiga-jigan siyasa sun sauya sheka, an saci mutane da yawa, Boko Haram ta galabaita amma taki karewa, an ceto wasu daga 'yan matan Chibok.Kusan rabin shekarar dai shugaban Najeriya M. Buhari bashi da lafiya, sai mukaddashin sa Faresa Yemi ne ya tafiyar da kasar.
Boko Haram ta sako wasu daga cikin matan Chibok.
Shugaban ya murumure ya dawo.
Ya kasa shiga Ofis saboda beraye.
Samarin Arewa sun so korar Kabilun kudu saboda Biafra
El-Rufai ya kori malamai 21,000
Har yau ba'a gama da Boko Haram ba, sun kuma kashe da yawa.
An nemi Nnamdi Kanu an rasa.

Atiku ya koma PDP.
Wata wai ta caka wa mijinta wuka ya mutu.
Suntai ya rasu.
Gwamnoni sun kasa biyan albashi.
An sauke Babachir da Oke na NIA, saboda badakalar satar kudade
Su P-Square mawaka tagwaye sun raba jiha.

No comments