Wani mahaifi ya dankarawa 'yar sa mai shekaru 10 ciki a jihar Legas

Share:

Wata kotun majistire dake zamanta a birnin Ikeja na jihar Legas, ta bayar da belin wani mahaifi Keneth Abuya, akan kudi Naira 500 000 bisa laifin dankarawa 'yar sa mai shekaru 10 ciki a duniya.

Alkaliyar kotun, B.O Osunsanmi, ta baiwa mahaifin wannan yarinya umarnin gabatar da mutum biyu da zasu tsaya masa a matsayin jingina tare da gargadin cewa sai sun kasance su na da mallakin kadara a jihar da kuma shaidar su ta biyan haraji.


Jami'in dan sanda mai shigar da kara, Mista Simeon Imhonwa, ya shaidawa kotun cewa, mahaifin yarinyar wanda mazaunin Egbeda ne ya saba kwakware 'yar ta sa da har yayi sanadiyar samar mata da juna biyu.

Yake cewa, mahaifiyar yarinyar ce ta shigar da kara a ranar 29 ga watan Nuwamba bayan da fuskanci lamarin da ake ciki, inda mahaifin yayi ikirarin buga wa 'yar ta sa kwalba idan ta furta wa wani mahaluki.

No comments