Wani ya kashe Mahaifiyar sa a wata Kasa bayan sun samu ‘dan rikici

Share:

Wani ya kashe Mahaifiyar sa a wata Kasa bayan sun samu ‘dan rikici

- Kwananaki wani Saurayi ya aika mahaifiyar sa lahira

- Yanzu haka Jami’an ‘Yan Sandan Kasar sun yi ram da shi
- Wannan saurayi ya datsewa uwar sa kai ya dauki bidiyo
A makon jiya mu ka ji labari cewa wani yaro ya kashe Mahaifiyar sa a Kasar Sin bayan sun samu rikicin da bai kai ya kawo ba a kwanaki kamar yadda Gidan BBC Hausa ta kawo rahoto. Sai daga baya ne aka san cewa an yi wannan kisar gilla.Ana zargin annan yaro ya kashe Mahaifiyar sa, ya kuma datse mata kai. Bayan yaron ya kashe Mahaifiyar ta sa, ya dauki bidiyo ya yada a shafin sa na WeChat. Wannan abu ya faru ne a Garin Wenxing da ke yankin Sichuan na Kasar Sin.

Maganar ta fashe ne kwanaki bayan abin ya faru inda abokin wannan yaro ya nunawa Mahaifiyar sa wannan bidiyo. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun yi bincike inda mu ka samu labari cewa kawo yanzu an kama wannan yaro da ake zargi da laifin kisa.

Kamar yadda rahoton Gidan BBC Hausa ya nuna, ‘Yan Sanda sun tabbatar da cewa an kama wannan yaro amma har yanzu ba ayi wani karin bayani ba. Yaron dai ya kashe mahaifiyarsa ne bayan da suka yi sa'insa a ranar Lahadi da daddare.

No comments