Zahra Buhari da mijinta sun cika shekara daya da aure

Share:

Masu iya Magana sunce soyayya da aure na da kyau amma sai dai zukatan da Allah ya kaddara da kasancewa tare ne zasu yi nasarar ganin kyawu da jin dadin dake tattare da zaman tare.


A watan Disamban 2016, Zahra Buhari da Ahmed Indimi sun ja hankulan mutane a yanar gizo bisa la’akari da Karin soyayyarsu, kudi da kuma mulki.
Daga Abuja zuwa Maiduguri, masoyan sun karade gurare da dama domin nuna soyayya na musamman da suke wa junansu. Yayinda mutane da dama ke taya ma’auratan murna, wasu suy addu’an samun irin wannan farin ciki yayinda wasu ke adawa.
Kamar a mafarki, kimanin kwanaki 365 kenan da ma’auratan suka zamo yan uwan juna ta hanyar auratayya. Wannan yasa NAIJ.com ta hado kan hotunan ma’auratan mai cike da so da kauna domin tunawa da wannan lokuta mafi tsada a rayuwar su.

1. A lokacin da suka halarci wani biki na daya daga cikin yan uwansu
2. Lokacin Sallar Idi a matsayin mata da miji
3. A lokacin taron bikin auransu
4. Lokacin zagayowar ranar haihuwar ta karo na 22 wanda yayi daidai da lokacin aurensu
5. Lokacin da suka tafi hutun shakatawa na musamman
6. Lokacin da suke kallon wani kogo mai ban sha'awa a kasar Spain
7. Lokacin da suke shirin raya sunnar ma'aiki cikin farin ciki

No comments