kannywood» Fati shu'uma Ta Baiwa Matan Yan Uwanta Sharawa Masu Sha'awa shiga Harka Fim

Share:
Shararriyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta baiwa dukkan masu sha'awar shiga a dama da su a harkar fina-finai musamman ma mata da su tabbata sun samu amincewar iyayen su tukuna.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da ita a gidan talabijin din nan na Hausa na Arewa24 a cikin shirin Ga Fili Ga Mai Doki na Kundin Kannywood tare mashiryin shirin Jarumi Aminu Shariff.

Jaruma ta soma da  cewa duk dai a cikin firar, jarumar ta kuma shawarci matan da su zama masu hakuri musamman ma da masoyan su da a kullum za su yi ta yin tururuwa domin kawowa gare su.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa jaruma Jamila Nagudu ce tafi burge ta a cikin jaumai mata sannan kuma Adam A. Zango ne yafi burge ta a cikin jarumai maza a masana'antar.

No comments