Labarai :- An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan kwayoyi

Share:
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa jarumin dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood da kuma na Kudu, Ali Nuhu ya samu babban matsayi. An dai nada jarumin ne a matsayin Jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi a karkashin gidauniyar “Big Church Foundation”

An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi Wannan dai ba shine karo na farko da jarumin ke samun irin wannan daukaka ba sakamakon tarin masoya da yake da shi. 

Ali Nuhu dai ya kasance daya daga cikin manyan jaruman fim din Hausa da zamaninsu ya haska a baya kuma yake kan haskawa, tauraron jarumin na haskawa tun zamanin da ya shiga masana’antar har izuwa yau. 

No comments