Kannywood: Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja

Share:
- Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja - Shin dan asalin jihar Kano ne - Mahaifiyar sa ba bahausa bace - Yana yin wakokin fina-finai, siyasa da kuma biki Kusan a iya cewa dukkan masu sha'awar harkokin fina-finan Hausa musamman ma mata sun san fitaccen mawakin nan watau Ado Gwanja. Shi dai Ado Gwanja a baya an fi ganin sa ne a cikin fina-finai a matsayin dan daudu amma kwatsam sai tauraruwar sa ta soma haskawa a fagen wakoki musamman ma na biki. Jarumin kuma fitaccen mawaki dai yana da matukar farin jini a tsakanin 'yan mata da ma matan aure domin irin salon kidan sa da yake yi. Yanzu dai a iya cewa matashin yana daga cikin wadanda tauraruwar su ke haskawa a farfaciyar masana'antar nishadantarwa a Kannywood. 

LATEST EPL 2018-19 POLITICS GOSSIP CELEBS WEDDINGS HAUSA NEWS ASK NAIJ Daga karshe: Babachir Lawal yayi magana karon farko bayan korar sa daga gwamnati Dandalin Kannywood: Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja Author: Mustapha Saddiq UPDATED: 9 HOURS AGO VIEWS: 1672 Category: Labarai - Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja - Shin dan asalin jihar Kano ne - Mahaifiyar sa ba bahausa bace - Yana yin wakokin fina-finai, siyasa da kuma biki Kusan a iya cewa dukkan masu sha'awar harkokin fina-finan Hausa musamman ma mata sun san fitaccen mawakin nan watau Ado Gwanja. Shi dai Ado Gwanja a baya an fi ganin sa ne a cikin fina-finai a matsayin dan daudu amma kwatsam sai tauraruwar sa ta soma haskawa a fagen wakoki musamman ma na biki. Jarumin kuma fitaccen mawaki dai yana da matukar farin jini a tsakanin 'yan mata da ma matan aure domin irin salon kidan sa da yake yi. Yanzu dai a iya cewa matashin yana daga cikin wadanda tauraruwar su ke haskawa a farfaciyar masana'antar nishadantarwa a Kannywood. Dandalin Kannywood: Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja Source: Facebook KU KARANTA: Auren wata jarumar fim din Hausa ya mutu kasa da wata 3 da daurawa Ga dai wasu daga cikin muhimman abubuwan da watakila baku sani ba game da jarumin, kuma mawaki: 1. Ana yi masa lakani da Limamin mata 2. Shi ruwa biyu ne, ma'ana; mahaifin sa bahaushe ne dan asalin Kano ne, mahaifiyar sa kuma Shuwa Arab ce 'yar asalin garin Maiduguri. 3. Waka ya fara kafin shiga harkar fim domin kuwa ya shafe shekaru akalla 12 yana yin waka amma ba'a san shi ba. 4. Yana da uban gida a harkar wata. Aminu Mai Dawayya shine uban gidan sa. 5. Yana yin wakar siyasa idan ya samu ba na biki kawai yake yi ba. 

No comments