kannywood › Wasu Daga Cikin Abubuwa Da Ya kamata ku Sani Game Da Fati Washa

Share:


Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta san ta
Jarumar tana daya daga cikin manayna jarumai mata da tauraron su ke haskawa a farfajiyar Kannywood.

An haife ta ranar 21 na watan Febreru na shekarar 1993.
Kwarerwar da kuma himma da take badawa a wajen aikin yasa tayi fice cikin yan matan Kannywood.

Wasu daga cikin tsoffin fina-finanta akwai Sarki, 'Yar Tasha, Ana Wata ga Wata, Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da, Gwaska returns sauransu.
Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba suna rigima ko kuma jan fada.

Kyakkyawar jaruma har yanzu bata yi aure ba amma akwai jita-jita da yadu shekarun baya cewa wasu daga cikin masana'antar Kannywood na neman ta da aure.

Daya daga cikin Nuhu Abdullahi ya bayyana cewa hakika yana son ta kuma zai so ta zama matar sa sai dai bai shirya yin aure ba.
Yace jarumar tana nuna masa biyayya kuma ta taimaka mashi sosai don haka yake matukar girmama ta.

Akwai jita-jita da take yawo akan Jarumar tana soyayya da jarumi Adam A Zango , duk dai basu fito fili sun tabbatar ko karyata hakan ba, Amma kowa ya yadda fati washa tafi kowace jaruma kusa da Adam A Zango domin tun daga fim din 'Sarki' har yanzu suna tare.
Tana kuma cikin fitattun jarumai dake da dinbim masoya masu binta a dandalin sadarwar zamani.

Tana da mabiya dubu shida da casa'in da daya a shafin ta na Instagram kana mabiyanta dubu saba'in da daya ne a Tuwita.
Jarumar ta samu lamban yabon da dama cikin gida har da wajen gida. Cikin jerin kyautar girmamawa da ta karba akwai City people awards.

Sources:pulsehausa

No comments