Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

Share:
Wani tsohon bidiyo ya zo hannun mu inda aka ji yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya rika tofawa tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso albarka a baya inda har ya nemi Allah ya sakawa Gwamnan da alheri. Magoya bayan Kwankwaso sun tuno da irin yabon da Shugaba Buhari da kan sa ya rika yi wa tsohon Gwamnan na Kano. Shugaba Buhari ya yabawa kokarin da Kwankwaso yayi wajen gina gidaje da kuma tituna da gadoji a Kano. Bayan nan Shugaba Buhari, ya kuma jinjinawa kokarin da Kwankwaso yayi wajen gyara harkar ilmi a Jihar Kano. Buhari ya yabawa Jami’o’in da Gwamnatin Injiniya Kwankwaso ta gina a lokacin mulkin sa a 1999 da kuma 2011. 

Buhari a wancan lokacin yake cewa duk wanda ya san Jihar Kano, lallai ta canza a lokacin Kwankwaso. Shugaba Buhari ya kara da cewa Injiniya Rabiu Kwankwaso ya nuna tattali wajen rikon Jihar Kano don haka sai dai a yaba masa.

No comments