Kannywood :- Shin Da Gaske Ne Ba Jituwa Tsakanin Nafisa Abdullahi Da Hadiza Gabon?

Share:

Shin Nafisa ta shirya da Hadiza Gabon?
An dade dai Nafisa na gaba da jaruma Hadiza Gabon.

Kuma duk da ba ta amsa tambaya game da dalilin da ya janyo sabani tsakaninsu ba, amma ta ce abu ne da ya faru kusan shekara daya da rabi, kuma ya riga ya wuce.

“Ba ni son sake dauko wannan zancen.”

A shekarar 2017 ne fitattun jaruman guda biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.

Nafisa ta ce babu wata dangantaka tsakaninta da Hadiza Gabon, bayan an tambaye ta ko suna kiran juna a waya.

“Ba mu cika haduwa da Hadiza Gabon ba, idan mun hadu muna dan gaisawa.”

1 comment: